14 Maris 2020 - 05:20
Matar Firai Ministan Canada Ta Kamu Da Coronavirus

Ofishin firaminsitan kasar Canada, ya sanar cewa matar firaministan kasar Justin Trudeau, cewa da Sophie Grégoire, ta kamu da cutar coronavirus.

(ABNA24.com) Ofishin firaminsitan kasar Canada, ya sanar cewa matar firaministan kasar Justin Trudeau, cewa da Sophie Grégoire, ta kamu da cutar coronavirus.

Sanarwar ta ce za a ci gaba da kebe matar, wacce ta ke ci gaba da daukar matakan da suka kamata, kuma shi ma firaministan kasar Justin Trudeau ya kebe kansa na tsawan mako biyu.

Nan gaba kuma za’a nemi mutanen da suka yi mu'amala da matar firaministan, amma ba za a yi wa Mista Trudeau gwajin cutar ba tukuna.

An dai dage duk wasu taruka da ya kamata Mista Trudeau ya halarta kwanan nan.

Kawo yanzu a kalla mutum 103 ne suke dauke da cutar a Canada, inda ta kashe Mutum guda.



/129